Kungiyar ‘yan kasa da shekara 20 ta Najeriya, Flying Eagles ta lallasa Keffi Selected da ci 7-0 a wasan sada zumunta da suka yi a Abuja ranar Asabar.
Wannan dai ita ce babbar nasara ta uku ga bangaren Ladan Bosso a wannan makon.
Kungiyar Flying Eagles da ta kafa sansani a Abuja a makon nan gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta matasa ‘yan kasa da shekaru 20 ta 2023, yanzu ta zura kwallaye 17 ba tare da an zura musu kwallo ba.
Dan wasan gaba na Niger Tornadoes, Emmanuel Jonas ya ci kwallaye uku rigis a wasan.
Sauran ‘yan wasan sun hada da Ridwan Seriki da Emmanuel Ekpeyong da Ibrahim Yahaya da Obiakor Ifesinachi.
A safiyar yau litinin ne ‘yan wasan Flying Eagles za su koma atisaye a filin FIFA Goal Project da ke Abuja.


