Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa, fiye da mutum dubu tamanin ne suka shiga kasar daga kasashen waje a matsayin ‘yan gudun hijira.
Shugabar hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Najeriya, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim ce ta bayyana hakan a tattaunawarta da BBC Hausa a yayin da ake bikin tunawa da Ranar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya, wato ranar 20 ga watan Yuni.
Ana bikin a kowacce shekara domin jawo hankalin jama’a kan mawuyacin halin da ‘yan gudun hijira suke ciki tare da wayar da kawunan jama’a kan ‘yancinsu.
Hajiya Imaan ta kara da cewa mutanen da suka shiga Najeriya sun fito ne daga kasashe talatin da hudu.