Kwamitin da babban Sufeton ‘yan Sandan Najeriya ya kafa ya gano cewa akwai fiye da mutum 300 da ke zaman jiran shari’a a wani gidan yarin jihar Kano ba tare da bayanan abubuwan da ake tuhumarsu ba.
Yayin ziyarar ba-zata da kwamitin ya kai ofisoshin ‘yan sanda da kotuna da kuma gidajen yari, ya gano abubuwa da dama da suke buƙatar a sake duba yadda ake tafiyar da su a fannin yadda ake tuhuma da gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata wani laifi.
Kwamitin ya fara aiki ne, bayan da shugaban ‘yan sandan ƙasar Mista Kayode Egbetokun ya kaddamar da shirin gyara ayyukan ‘yan sanda a baya-bayan nan, sakamakon kafa wata dokar ‘yan sanda da ake kira ‘Force order number 20’, ta yadda aikin jami’an zai zamo dai-dai da yadda aikin dan sanda abokin kowa ke gudana a duniya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Hussaini Muhammad Gumel shi ne shugaban kwamtin a Kano, tare da wakilcin ɓangaren shari’a da ‘yan kungiyoyi da lauyoyi da kuma masu rajin kare hakkin dan adam, ya kuma ce sun fara zuwa caji-ofi-din ‘yan sanda ne tun da farko, inda suka gano abubuwa da dama.
Kazalika, CP Hussaini Gumel, yace sun kuma ziyarci kotuna, inda suka tattauna da alkalai da masu gabatar da kara, inda ya cenan gaba za su hadu da mambobin kwamitin, inda za su tattara bayanan da suka samu wuri guda, sannan su fitar da rahoto daya kana a mika wa hukumomin da abin ya shafa don daukar mataki na gaba.
Bayanai na cewa ana-sa-rai, sauran kwamishinonin ‘yan sandan jihohin Najeriya ma, za su bi sahun jihar Kano, wajen gudanar da irin wannan bincike, da nufin gyara yadda aikin ‘yan sanda da bangaren shari’a da gidajen yari suke aiki.
A kwanakin baya ne gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya ta hanyar biya wa masu kananan laifuka tara da yi wa wasu afuwa, sai dai kawo yanzu babu bayanin ko shirin ya ci gaba bayan da aka kaddamar da shi a jihar Kano.