fidelitybank

Fiye da mutane 30 ne su ka mutu bayan motar Ɗangote ta aka kan motoci

Date:

Rundunar ƴansandan babban birnin Najeriya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida da ƙonewar motoci 14 bayan wata babbar mota ta kama da wuta a yankin Karu.

Kakakin rundunar ƴansandan SP Josephine Adeh wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce ibtila’in ya faru ne a jiya laraba da ƙarfe 6:58 na yamma bayan wata babbar mota da ke maƙare da siminti ta ƙwace ta faɗa kan motocin da ke maƙale cikin cunkoso ababen hawa kusa da gadar Nyanya.

Ta ce ma’aikatan ceto sun yi gaggawar isa wurin da ke cike da baƙin hayaƙi da tsananin zafi domin ceto waɗanda suka maƙale inda ta ce an samu nasarar zaƙulo mutane shida, sai dai bayan kai su asibiti likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Kakakin rundunar ta kuma ce tare da haɗin gwiwar ƴansanda da ma’aikatan kashe gobara da ma wasu jam’ian tsaro an samu nasarar kashe gobarar.

Rundunar ƴansandan Abuja ta kuma miƙa ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda iftila’in ya shafa tare da tabbatarwa da alumma cewa za a gudanar da cikakken bincike kan sanadin iftila’in da kuma yadda za a kare sake afkuwar irinsa.

Sai dai a cewar jami’an VIO, babbar motar kaya ta Kamfanin Dangote mai amfani da iskar gas da ke ɗauke da siminti ta afka kan motoci fiye da 14 kuma ta kashe mutum aƙalla 30 a jiya Laraba a Abuja.

Kwamandan jami’an VIO a yankin Kugbo, Shehu Dalhatu ne ya shaida hakan.

nigeria peace corps

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp