fidelitybank

Fiye da Mutane 26 na hannun ‘Yan Bindiga a Zamfara

Date:

‘Yan bindigar da suka mamaye garin Sabon Gari a ƙaramar hukumar Ƙaurar Namoda sun kashe aƙalla mutum uku tare da yin garkuwa da 26 da suka haɗa da mata da yara ƙanana.

Maharan da jaridar Daily Trusta ruwaito cewa magoya bayan ɗan bindigar nan ne Bello Ƙaura da aka fi sani da Ɗan Sade, da ake ta’allaƙawa da munanan hare-haren da suka addabi ƙananan hukumomin Ƙaurar Namoda da Maradun.

Rahotannin sun tabbatar da cewa mazauna garuruwan Kungurki da Sabon Gari da Uguwar Sarkin Musulmi da Unguwar Rogo da Yamatsiwa sun tsere daga gidajensu domin gujewa hare-haren ‘yan fashin dajin.

A ranar Jumu’a ma wasu ‘yan bindiga sun kashe aƙalla mutum huɗu a yankin ciki har da sakataren ƙaramar hukumar Birnin Magaji inda nan ma wasu maharan suka yi garkuwa da ƙarin wasu mutum biyu.

Majalisar dokokin jihar Zamfara dai a baya ta bayana fatan hukumomin sojojin ƙasar su kai wa ƴanfashin hari cikin sansanoninsu da ke dajin Gando da ƴarjiji da Mazaro, kamar yadda a baya a ka kai hari kan sansanonin ƴan bindigar a dazukan Zurmi da Tsafe tare kuma da sanya shingayen binciken jami’an tsaro tun daga Mayinci har zuwa garin Gummi.

Jihar Zamfara dai na sahun gaba cikin jerin jahohin arewa maso yamma da ke fama da harin ‘yan bindiga waɗanda kisan jama’a da ƙona amfanin gona tare da garkuwa da mutane.

sani ahmad

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp