Ƙungiyar Likitoci ta ‘Medecins sans frontieres’ ta ce fiye da masu raunuka 20,000 ne ke maƙale a Gaza.
Jami’an Masar sun ce ‘yan ƙasashen waje 335, da masu tsananin raunuka ko jinya 75 ne aka shigar ƙasar domin yi musu magani ta kan iyakar Rafah a ranar Laraba.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce an ga motocin ɗaukar marasa lafiya ɗauke da majinyata a harabar asibitocin Masar.
To sai dai ƙungiyar MSF ta yi kira da a ƙara adadin masu raunukan da ake kwashewa, da kuma kiran tsagaita wuta tare da shigar da ƙarin kayan agaji zuwa Gaza, inda ake cikin tsananin buƙatar tallafi.
“Na kaɗu da yadda kowa ke tambayar abinci, da ruwan sha,” in ji Philippe Lazzarini, wani babban jami’an MDD da aka bari ya shiga Gaza tun bayan fara yaƙin.