fidelitybank

Fiye da kashi 1 cikin 4 masu cutar zazzaɓin cizon sauro a Najeriya su ke – Hukumar Lafiya

Date:

Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce, fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na masu fama da cutar zazzaɓin cizon sauro a duniya, a Najeriya suke.

Daraktar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) shiyyar Afirka, Dakta Matshidiso Moeti ta ce yawan al’ummar Najeriya, ya zama ƙalubale ga matakan da ake ɗauka na rage bazuwar zazzaɓin cizon sauro da ake fama da shi a Najeriya.

Ta bayyana hakan ne a Abuja yayin babban taro da wani babban jami’in shirin Amurka na kakkaɓe cutar maleriya a duniya, Dakta David Walton, da babban jami’in Amurka kan shirin daƙile cuta mai karya garkuwar jiki a duniya, Dr. John Nkengasong da sauransu.

Dakta Moeti ta ce “Nahiyar Afirka na da kaso mafi yawa na masu fama da zazzabin cizon sauro a duniya, wanda ya kai kusan kashi 95 cikin 100 na masu cutar, kuma shi ne yake da kashi 96 cikin 100 na waɗanda suka mutu sanadin zazzabin cizon sauro a shekarar 2021.

“Yayin da Najeriya ke da kusan kashi 27 cikin 100 na masu cutar zazzaɓin cizon sauro a duniya, duk da haka ƙasar ta samu gagarumin ci gaba.

“Yawan masu fama da cutar zazzaɓin cizon sauro sun ragu da kashi 26 cikin 100 tun daga shekara ta 2000, wato daga masu kamuwa da zazzaɓin 413 a cikin duk mutum 1,000 zuwa masu kamuwa 302 a cikin duk mutum 1000 a shekara ta 2021.

Haka zalika, mace-mace sanadin cutar zazzaɓin cizon sauro sun ragu da kashi 55 cikin 100, daga kashi 2.1 a cikin mutum 1000 zuwa kashi 0.9 a cikin mutum 1000.”

Moeti ta jaddada muhimmancin samun cikakkun bayanai don jagorantar matakan riga-kafin cutar maleriya da kawar da ita.

Ta kuma jaddada bukatar samar da muhimman bayanai kan yanayin cutar a kowacce jiha ta Najeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Ta ƙara da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya za ta ci gaba da jajircewa wajen ba da gagarumar gudunmawar haɗin gwiwa tare da gwamnatin Najeriya da cibiyoyin samar da kuɗi da abokan ƙawance a Najeriya don inganta zuba kuɗi a fannonin da za su taimaka wajen rage yawan cutar maleriya da sauran cutuka a ƙasar.

A yayin taron, ministan lafiya da walwalar jama’a na Najeriya, Farfesa Ali Pate, ya yaba wa Amurka da sauran abokan huldarsu wajen zuba kuɗi har dala miliyan 900 a shirye-shiryen yaki da cutar zazzabin cizon sauro da cuta mai karya garkuwar jiki da kuma tarin fuka a Najeriya

sun news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp