Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya sauka a Tel Aviv na ƙasar Isra’ila a yau Alhamis.
A daren jiya ne ya tashi zuwa Cyprus sannan kuma ya wuce Tel Aviv a safiyar yau.
Yanzu Sunak zai nufi birnin Kudus domin ganawa da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da shugaban Isra’ila Issac Herzog a cikin ‘yan sa’o’i masu zuwa.
Rishi Sunak ya shaidawa manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Tel Aviv cewa harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba “aikin ta’addanci ne da ba za a iya cewa komai ba”, kuma ya nanata cewa Birtaniya na goyon bayan Isra’ila.
Sunak ya ce “Ina matukar fatan ganawar da na yi daga baya tare da Firayim Minista da shugaban kasa kuma ina matukar fatan za su kasance tarurruka masu amfani,” in ji Sunak.


