Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya gana da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a ziyararsa ta farko zuwa Ukraine tun bayan hawansa mulki.
An yi ganawar ne domin ‘tabbatar da goyon bayan Birtaniya ga ƙasar Ukraine’ kamar yadda mai magana da yawun fadar Firaminsitan Birtaniya ya tabbatar.
”Mun tattauna batutuwa masu muhimmanci ga ƙasashenmu biyu da kuma batun tsaro da duniya ke fuskanta” kamar yadda Mista Zelensky ya wallafa a shafinsa na Telegram.
Ya ƙara da cewa “Muna da ƙarfi kuma za mu cimma burin da muke so”
Mista Sunak ya ce ya ji daɗin ziyara tasa zuwa Kyiv, ya kuma alkawarta cewa Birtaniya za ta ci gaba da goya wa Ukraine baya a yakin da take yi.
A lokacin ganawar mista Sunak ya ce Birtaniya za ta samar da tallafin kuɗi domin taimaka wa sojojin saman Ukraine wajen kare fararen hula da kuma ababen more rayuwa na ƙasar daga hare-haren Rasha.
A ‘yan watannin baya-bayan nan dai Ukraine na kiraye-kirayen neman tallafi daga ƙasashen yamma, domin kare kanta daga hare-hare ta sama da Rasha ke ƙaddamarwa a fadin ƙasar.