Firaiministar Denmark, Mette Frederiksen ta ji ciwo a wuya bayan wani mutum ya kai mata hari tana cikin tafiya a ƙasa, a tsakiyar birnin Copenhagen.
Wani mutum ne ya nushi ƴar siyasar a daidai lokacin da take tattaki a birnin.
Tuni aka kama mutumin da ya kai mata harin kuma zai bayyana a gaban kotun Frederiksberg domin amsa tuhumar da ake masa.
Wannan hari na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan an harbi Firaiministan Slovakia Robert Fico, yayin da yake gaishe da magoya bayan sa. In ji BBC.
Shugabar tarayyar Turay, Ursula von der Leyen ta bayyana harin a matsayin mummunan aiki da ya saɓa duk wata hanyar kirki da nahiyar Turai ta amince da ita.