Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce, ya ji takaicin abin da shugaban hukumar zaɓe na Jihar Farfesa Hudu Yunus Ari, ya yi na ayyana abokiyar takararsa a matsayin wadda ta lashe zaɓen jihar tun gabanin a kammala tattara sakamako.
Ya ce tuntuni sun yi hasashen hakan zai iya faruwa, shi yasa suka yi ƙorafin a cire shi daga harkokin gudanar da zaɓen domin ba zai yi musu adalci ba, domin sun ga abin da ya faru a Sokoto.
“Shi yasa muka yi ta kira ga INEC ta cire shi, saboda mun ga abin da wancan ya yi a Sokoto, muka yi fargabar kada ya yi mana a nan.
“Sun yi abin da ya kamata domin jiya sun cire shi sun kawo kwamishina wanda shi ya aiwatar da ayyuka yadda ya kamata,” in ji gwamna Fintiri.
Ya ce abin mamakin shi ne Farfesa Hudu ya je cikin mutane yana cewa “bai ji daɗi ba da aka cire shi jiya ba, amma yau zai aikta abin da yake so,”.
A cewarsa “Babu sakamako a hannunsa babu takarda cewarsa kawai ya ba wa wance ta ci zaɓe,” abin da ya bayyana a matsayin abin takaici.
Fintiri ya yaba wa INEC kan matakin da ta ɗauka cikin gaggawa, na dakatar da karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta Adamawa.


