Gwamna Umar Finitiri ya bayyana mace ta farko a matsayin mataimakiyar gwamna a yankin arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Kaletapwa George Farauta a Yola.
Bikin kaddamarwar wanda ya jawo dubban kungiyoyin mata ya gudana a gidan gwamnati a yau, Laraba.
Fintiri ya ce, zaben Farfesa Farauta ya samo asali ne, sakamakon bincike mai zurfi da kuma amincewar mataimakin gwamna mai ci, Crowther Seth.
Da yake jaddada cewa “Na yi aiki tare da ita a matsayin mai ziyara a Jami’ar Jihar Adamawa, na gwada ta kuma ta tabbatar da cewa ta kasance amintacciya, kamar mataimakin gwamna, Crowther Seth.”


