Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa, ya sanar da haramta sarewa da kona kututtukan itatuwa domin yin gawayi a jihar.
Gwamnan ya fada a ranar Alhamis cewa daga yanzu za a fara aiki da dokar da aka kafa ta hana sare bishiya da yin amfani da kututturen bishiya wajen samar da gawayi wajen dafa abinci.
Fintiri ya bayar da wannan umarni ne a karon farko a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya da suka yi masa mubayi’ar Sallah daga sassan jihar sannan kuma ga ‘yan majalisar dokokin jihar da suka ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Yola a fadar gwamnati da ke Yola a lokacin bikin Sallah.
Ya shaida wa ‘yan majalisar da ke karkashin jagorancin kakakin majalisar, Bathiya Wesley, cewa dukkansu suna da alhakin tabbatar da bin dokar da ta hana yanke bishiyu.
“Mun cimma matsaya mai karfi na cewa kada a rika sare itatuwa da kuma samar da gawayi. Ana sa ran dukkanmu mu taka rawar gani wajen ganin an aiwatar da dokar hana sare itatuwa da ba mu aiwatar da ita daga yanzu ba. Na fada wa sarakunan gargajiya a lokacin da suka zo.
“Dole ne dukkanmu mu yi abin da ya kamata mu yi ta bangarenmu ta wannan hanyar. Dole ne mu karfafa wa jama’armu gwiwa su koma hanyar da za ta dore a madadin gawayi.”
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yanke shawarar yin tsayin daka kan sare itatuwa galibi don konewa da kuma samar da gawayi saboda an gano sare itatuwa ya haifar da ambaliyar ruwa a fadin jihar.
“Mun ga wuraren da ba a samu ambaliyar ruwa ba a yanzu ana yawan ambaliya, suna haddasa lalata ga gonakinmu, gidaje da kadarori masu kima,” in ji shi.