Finidi George na iya shirin komawa gasar firimiya ta Najeriya, NPFL, bayan ya yi murabus a matsayin kocin Super Eagles.
Ya sauka daga mukamin ne bayan kwanaki 40 kacal saboda takun saka da hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF.
Duk da haka, Rivers United na tunanin Finidi ya zama sabon kocin su, a cewar Nation.
Kulob din NPFL yana son yin sauye-sauye bayan kammala kakar wasa mara kyau.
Rivers United dai ta fara kakar bana da kyau, inda ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyoyi na CAF kafin daga bisani USM Alger ta Algeria ta fitar da ita.
Duk da haka, sun yi gwagwarmaya a gasar, inda suka kare a waje da matsayi na farko kuma sun kasa samun tikitin nahiya a karon farko cikin shekaru uku.