Hukumar ƙwallon kafa ta duniya Fifa ta ce tana son ‘yan wasa su dinga ɗaga hannunsu sannan su haɗa su wuri guda a matsayin wata alama da za ta nuna an yi wariyar launin fata yayin wasa.
Manufar daga hannun ita ce shaida wa alkalin wasa an yi abin da ya saba ka’ida domin ya dauki mataki.
Wannan daya ne daga cikin matakan da Fifa take dauka domin yaki da nuna wariyar launin fata.
Shugaban Fifa Gianni Infantino ya ce, babu wani dalili da zai sa su nuna wariya ga wani saboda launin fatarsa, idan kasashen duniya ba za su iya magance hakan ba, su za yi kokari a fannin kwallon kafa.