A ranar Alhamis ne kotun Turai ta yanke hukunci a kan Super League da FIFA da UEFA ke kokarin dakatar da su.
Kotun ta ce hukumomin kwallon kafa biyu ba za su iya yin amfani da karfinsu ba, su hana kafa sabuwar gasar ko kuma haramta kungiyoyin da ke shirin shiga gasar.
“Ikon FIFA da UEFA ba su da irin wannan sharudda, saboda haka, suna cin zarafin matsayi mafi girma. Haka kuma, idan aka yi la’akari da yanayinsu na son zuciya, dole ne a kiyaye dokokinsu kan amincewa, sarrafawa da kuma takunkumi don zama hani mara tushe kan ’yancin samar da ayyuka, ”in ji sanarwar a wani bangare.
“Hakan ba yana nufin dole ne a amince da wata gasa irin ta Super League ba. Kotu ba ta yanke hukunci kan takamaiman aikin a cikin hukuncinta.
FIFA da UEFA sun yi zargin cewa A22, masu goyon bayan Super League, sun karya doka.
Sai dai hukuncin da babbar kotun Turai ta yanke a yau ya ci gaba da kasancewa a kansu.
Ku tuna cewa Real Madrid da Barcelona ne kawai kungiyoyi da suka rage daga kungiyoyi goma sha biyu da suka hada karfi da karfe wajen kafa sabuwar Super League.
Kungiyoyin Manchester City, Arsenal, Chelsea, Liverpool, Tottenham Hotspur, Manchester United, Atletico Madrid, Inter Milan, Juventus da AC Milan suma sun shiga, amma sun fice daga teburin jim kadan bayan magoya bayansu sun nuna rashin amincewarsu da hakan.


