Lauyan, Femi Falana, SAN, ya bayyana yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci ministocin da ke da ruwa da tsaki a harkokin siyasa tare da korarsu amma suka kasa mika wasikunsu na murabus.
Ku tuna cewa ofishin yada labarai na kwadago da samar da ayyukan yi ya yi watsi da ikirarin da Falana ke yi na cewa Ministan, Chris Ngige ya janye takardar murabus dinsa ne bayan kammala zaman tattaunawa da shugaban kasa, Buhari a ranar Juma’ar da ta gabata.
A wata sanarwa da ofishin ya fitar a Abuja, ofishin ya ce, ministan bai rubuta ko mika takardar murabus ba, inda ya kara da cewa “Falana yana kunyata jama’a da mummunar girbi na tunaninsa.”
Lauyan Falana ya caccaki Ngige da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, na watsi da burinsu na siyasa a zaben 2023 domin ci gaba da zama a majalisar ministocin Buhari. A cewar Vanguard.