Jami’an hukumar leken asiri ta tarayya reshen rundunar ‘yan sandan Najeriya sun kama Oriyomi Hamzat, mai gidan rediyon Agidigbo FM.
Gidan rediyon ya tabbatar da faruwar lamarin ta wata sanarwa da aka fitar a safiyar ranar Alhamis.
Sanarwar daga Agidigbo FM tana cewa: “Muna ta fama da kiraye-kirayen da sakonni tun da sanyin safiyar yau biyo bayan damuwar da ‘yan Najeriya masu kishin kasa a gida da waje, abokan aikinmu na kafafen yada labarai da sauran jama’a ke yi game da lafiyar shugabanmu na Sure Etiquette Media Plus Ltd. uwar kamfanin na Agidigbo FM, Ibadan, Agidigbo FM, Lagos da Agidigbo Television, Mr. Oriyomi Hamzat.
“Don haka za mu so mu yi amfani da wannan kafar wajen sanar da kowa cewa, a kwanakin baya wasu jami’an tsaro da dama sun yi wa Mista Oriyomi Hamzat gayyata tare da yi masa tambayoyi, ciki har da hukumar leken asiri ta jihar (SIB) kadai; duk wanda ya girmama tare da halarta.
Tambayoyin dai bai rasa nasaba da kiran da ya rika yi na a yi taka-tsan-tsan a shari’ar da ake yi wa Cif Rahman Adegoke Adedoyin kan mutuwar Timothy Adegoke wanda ya rasu a wani yanayi na rashin jin dadi a otal din da ke jihar Osun. A cewar PM News.