Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa, jami’an hukumar FBI mai binciken manyan laifuka, sun kai wani samame gidansa da ke Jihar Florida, kuma sun balla wani akwatin ajiyar kaya da kudade da ke cikin gidan nasa.
Daga baya wani dan tsohon shugaban, Eric Trump ya shaida wa tashar talabijin ta Fox News cewa, binciken da aka gudanar a gidan mahaifin nasa da ke Mar-a-Lago na da alaka da wasu takardu da ofishin adana takardun tarihi na Amurka ke nema ne.
Har zuwa wannan lokacin, hukumar ta FBI da ma’aikatar Shari’a ta Amurka ba su ce uffan ba. In ji BBC.
Cikin Wata sanarwa, Donald Trump, wanda na Jihar New York yayin da aka kai sumamen, ya ce, an yi wa “gidana na Florida kofar rago”, saboda samamen da wasu jami’an FBI msu yawa suka kai.