Shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum, ya ce ƙasarsa da Birtaniya na da babbar alaƙa, kasancewa a shekarun baya-bayan na Birtaniya ta buɗe ofishin jakadanci a ƙasar domin ƙarfafa zumunci tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ƙara da cewa ya je bikin naɗin sarki Charles lll ne sakamakon kyakkywar alaƙar da ke tsakanin masarautar Birtaniya da ƙasashen Afirka.
Shugaba Bazoum ya ce yana fatan sabon sarkin ya yi koyi da mahaifiyarsa wajen riƙe ƙasashen Afirka a zuciyarsa.