Rundunar ‘yan sandan jihar Plateau, ta kama wani fasto bisa zargin yin garkuwa da kansa domin karɓar kuɗi a wajen mabiyansa.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar ta ce Faston mai suna Albarka Bitrus ya haɗa baki da wasu ne ya ɓoye kansa domin ya karɓi kuɗin fansa a wajen mabiyansa.
Sanarwar ta ce an kama faston tare da waɗanda ya haɗa hannu da su wajen aikata wannan laifi bayan da suka samu bayanan sirri da ke cewa tuni mabiya cocin suka biya naira 600,000 a matsayin kuɗin fansa.
“Bayan samun labarin garkuwa da faston, da biyan nairan 400,000 da 200,000 daban-daban a matsayin kuɗin fansa domin sakinsa, sai lamarin ya fara bai wa mutane shakku” kamar yadda sanarwar ‘yan sandan ta bayyana
Sanarwar ta ci gaba da cewa ”Bayan samun bayanan sirri, sai baturen ‘yan sanda na Nassarawa Gwong ya gayyaci faston, nan take aka fara gudanar da bincike, inda kuma faston ya tabbatar da cewa ya haɗa baki ne da wasu ne domin ya karɓi kuɗi a wajen mabiyansa”.