fidelitybank

Fasto a Amurka zai shafe shekaru 14 a kurkuku

Date:

Wata kotu a Jihar Georgia da ke Amurka ta yanke wa wani mai wa’azin Kirista zaman gidan yari na shekara 10 bisa laifin yi wa wata yarinya ‘yar Uganda mai shekara 14 fyade.

Faston ya aikata laifin ne a lokacin da yarinyar ke karkashin kulawarsa a majami’ar Orthodox Presbyterian da ke yankin gabashin Mbale a Uganda.

Bayan zaman gidan sarka da Eric Tuininga mai shekara 45 wanda fito daga garin Milledgeville da ke jihar Georgia zai yi a kurkukun Amurka, zai kuma biya tarar dala dubu 20 da za a bai wa yarinyar.

Sannan zai shafe duka rayuwarsa bayan sakin sa daga kurkuku a matsayin wanda hukuma take lura da shi da yi masa lakabi a matsayin wanda ya taba gudanar da cin zarafin jinsi.

Dan mishan din wanda ya yi zaman wakafi yayin da ake shari’ar, ya amsa laifinsa a watan Fabrairun wannan shekara.

Kamar yadda wata sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta nuna, wani Ba’amurke ne mai alaka da majami’ar Orthodox Presbyterian da ke zaune a Mbale ya tuntubi ofishin jakadancin Amurka a watan Yunin 2019 domin kai karar Tuininga. In ji BBC.

Ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta binciki zargin, tare da taimakon ma’aikatar harkokin wajen Amurkar da Ofishin Tsaro na Diflomasiyya (DSS) da ke birnin Kamfala a Uganda.

punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp