Fasinjojin jirgin kasa da`yan bindiga suka sace a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ke cika kwana 100 a hannun maharan.
Fiye da mutum hamsin ne, ake kyautata zaton suna hannun `yan bindigar, ciki har da mata da kananan yara, kuma tun lokacin da aka sace su mahukunta ke ikirarin daukar matakan kubutar da su amma har yanzu haƙa ba ta cimma ruwa ba.
Dangi da abokan arzikin wadanda aka sacen sun yanke shawarar gudanar da zanga-zangar lumana don jan hankalin mahukunta game da halin da `yan uwansu ke ciki.
A karshen watan Maris din da ya wuce ne `yan bindigan suka kai hari kann jirgin kasan, inda suka kashe mutum takwas daga cikin fasinjojin da ke ciki kana suka kama mutane da dama suka tafi da su. Kodayake daga baya sun saki wasu bisa dalilai na jinkai kamar yadda `yan bindigan suka yi ikirari a cikin wani bidiyo. Amma wasu rahotanni na cewa sun karbi miliyoyin naira kudin fansa.