Fasinjoji da dama ne suka kone kurmus a wani hatsarin mota da ya afku a yammacin ranar Juma’a a garin Ode-Omu na jihar Osun.
Kakakin hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC reshen jihar Osun, Agnes Ogungbemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne a sakamakon karon da motocin biyu suka yi.
Ogungbemi ya kuma bayyana cewa daya daga cikin motocin na dauke da kwalabe na Liquiified Petroleum Gas, LPG wanda aka fi sani da iskar gas.
Ta ce gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar kwalaben gas din da motocin biyu suka yi.
Ba a iya tantance adadin wadanda suka mutu amma kakakin hukumar FRSC ta Osun ya bayyana cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu.
A nata jawabin, “Babu cikakken bayani a yanzu saboda ba mu iya gano wadanda suka mutu ba amma an kai wadanda suka jikkata zuwa cibiyar kiwon lafiya ta Ise Oluwa Odeomu.
“Daya daga cikin motocin dauke da iskar gas, ta fashe kuma ta haddasa gobarar.”