Fasinjoji da ke cikin wani jirgi a Australia sun yi nasarar fin karfin wani matashi da ya shiga jirgin ɗauke da bindiga.
Rahotanni na nuna cewa matashin mai kimanin shekara 17 ya shiga ne bayan ya tsallako ta wani shinge a filin jirgin sama na Avalon da ke kusa da Melbourne.
Bidiyon da aka wallafa a shafukan intanet na nuna lokacin da ma’aikatan jirgin suka buge bindigan daga wurin yaron.
Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ne ya riƙe shi ta kai har lokacin da jam’ian ƴansanda su ka iso.