Rahoton da ke zuwa mana na nuni da cewa, akalla fasinjoji goma sha shida ne suka bace, sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a ranar Asabar, 9 ga watan Yuli, 2022 a unguwar Ojo da ke jihar Legas.
Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas (LASWA), a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta sanar da cewa, jirgin ya taso ne daga Mile 2, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Ibeche a axis Ojo.
Sanarwar ta kara da cewa, “da misalin karfe 7.45 na yammacin ranar 8 ga watan Yuli, 2022, hukumar kula da hanyoyin ruwa ta jihar Legas da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa ta samu kiran da ya faru a magudanar ruwa.
A cewar sanarwar, kyaftin din ya karya ka’idojin hanyar ruwa yayin da yake tafiya da maraice ba tare da rigar ceto ga fasinjoji ba.