Wani jirgin sama na fasinja mallakin kamfanin Overland Airways ya kauce wa wani mummunan hadari a ranar Laraba yayin da yake dauke da fasinja 33 daga Ilori zuwa Legas.
Kamfanin Overland ya ce hadarin ya auku ne saboda “wani matsanancin zai a daya daga cikin injinansa”.
Tashar Channels Television ta wallafa a shafinta cewa kamfanin na Overland ya ce “wannan lamarin ya faru ne yayin da jirgin ke shirin sauka, sai dai jirgin ya sauka babu matsala.”
Sanarwar kamfanin ta kuma ce, “Dukkan fasinjojin jirgin 33 sun sauka daga jirgin a tsanake kamar yadda aka saba a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke birnin Legas.”
Babu rahoton wani daga cikin fasinjojin da ya sami rauni.