Hukumar kukla da wutar lantyarki ta Najeriya, NERC, ta dora alhakin lalacewa babban layin lantarkin ƙasar kan fashewar wata taransifoma a tashar rarraba lantarki ta Jebba.
Da safiyar ranar Asabar ne mafiya yawan sassan ƙasar suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki, karo na uku cikin mako guda.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X ta ce ta damu matuƙa kan halin da ka shiga na lalacewar babban layin lantarkin.
”Daga bayanan da muka samu, mun gano cewa matsalar da aka samu yau,. ta faru ne sakamakon fashewar wata taransifoma a tashar rarraba lantarki ta Jebba, wanna shi ne dalilin da ya haddasa lalacewar babban layin amu”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Hukumar ta kuma ce jama’anta na nan suna aiki ba ƙaƙƙautawa don ganin sun gyara komai, domin maido da wutar, ba tare da daukar dogon lokaci ba.