fidelitybank

Fasa Kauri: Kwastam ta kama kayan sama da Naira miliyan 854 a Kano

Date:

Hukumar hana fasa kauri ta kasa Kwastam, ta kama haramtattun kayayyaki da su ka kai sama da Naira miliyan 854 a cikin watanni Uku.

Mataimakin Kwanturola, Oseni Olorukooba, kodinetan hukumar kwastam mai kula da jihohin Kano da Jigawa, ya bayyana cewa masu fasa kaurin a yanzu ba su da wata mafaka da za su kai ga aikata muggan laifuka.

Ya ce,”Kayayyakin da a ka kama sun hada da motoci biyu, buhunan shinkafar kasar waje 413 da kuma bale 382 na kayan sawa. Sauran sun hada da katan 150 na macaroni, katon spaghetti 200, katuna 638 na takalman kasashen waje masu girma dabam na yara, maza da mata”.

Ya bukaci kafafen yada labarai da su ci gaba da fadakar da jama’a kan illolin da ke tattare da safarar kayayyakin da aka haramta a cikin kasar nan.

Ko’odinetan ya kuma jaddada aniyar rundunar na yaki da fasa kwauri.

Olorukuba ya kuma yabawa jami’an hukumar da kuma jami’an hukumar bisa samun nasarorin da a ka samu a tsawon lokacin da a ke bitar.

legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp