Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa ‘yan Ukraine da suka tsere daga gidajensu, saboda yaƙin da ake yi na fuskantar ƙarancin mai da kuɗi da kayan kula da lafiya.
BBC ta rawaito cewa, mutane da yawa ne ke ta gudun tsira, kafin dakarun Rasha da suke durfafawo su kai ga inda suke.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, ta yi kiyasin cewa kusan mutum 100,000 tuni sun rabu da gidajen, amma kuma hukumar na ganin wasu mutanen kusan miliyan biyar za su yi kokarin ficewa daga kasar zuwa waje yayin da fadan ke kara rincabewa.
Ministan harkokin waje na Hungary ya ce, akwai dogayen layukan motoci, da su kai tsawon kilomita biyar a kan iyakar kasarsa da Ukraine da Poland.
Kuma ta ce tuni mutum kusan 29,000 sun riga sun tsallaka cikinta daga Ukraine a jiya Alhamis.


