Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya naɗa tsohon shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Attahiru Jega a matsayin mai ba shi shawara na musamman sannan kodinetan shirin shugaban ƙasa na kawo sauyi a harkar kiwon dabbobi.
Cikin sanarwar naɗin da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar da maraicen ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya ce yana fatan naɗin zai kawo gagarumin sauyi mai ma’ana a harkar kiwon dabbobi a ƙasar domin ƙarfafa burin shugaban na gina ƙasar.
Dama dai Farfesa Jega tare da Tinubu sun jagoranci kwamitin shugaban ƙasa kan inganta harkokin kiwo.
”Kwamitin ya kuma gabatar da cikakken rahoto da shawarwarin inganta harkokin kiwo a ƙasar nan, ciki har da shawarar kafa hukumar kula da kiwon dabbobi da a yanzu haka ke da minista”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Farfesa Jega mai shekara 68 – wanda tsohon shugaban Jami’ar Bayero ta Kano ne – ya jagoranci hukumar zaɓen Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015.