Dillalan man fetur ta ƙasa IPMAN, sun ce, farashin man fetur ya ƙaru zuwa naira 720 a kan lita ɗaya daga naira 651, a wani lamari da ya sanya tashoshin sauke mai suka kasance tamkar babu kowa
Wannan a cewar dillalan man ya samo asali ne daga yawan sauyin da ake samu na darajar kuɗaɗen waje.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa dillalan man fetur su ma sun bayyana cewa gidajen mai da dama na rufewa a kullum yayin da kasuwar sayar da mai ke ƙara tabarbarewa.
Sun ce hakan na iya haifar da matsalar karancin man fetur a cikin watanni masu zuwa.
Da yake jawabi a wurin taron shugabannin kungiyar masu samar da man fetur da iskar gas ta Najeriya, a Abuja ranar Alhamis, shugaban ƙungiyar, Benneth Korie, ya ce a halin yanzu harkoki sun tsaya a tashoshin sauke man fetur masu yawa.
Shi ma shugaban kamfanin PETROCAM Trading, Patrick Ilo da yake zantawa da jaridar, ya bayyana cewa kudin man fetur da suka shigo da shi metrik tan 52,000 a ranar Talata, ya kai naira 720 duk lita daya ba tare da tallafin hukuma.
A cewarsa, matukar farashin man fetur ya kai naira 720 duk lita daya a tashoshin sauke man fetur, to mai yiwuwa ne kudin lita daya zai iya kai wa naira 729 a gidajen mai na jihar Lagos, idan gwamnatin Najeriya tabbas ta dakatar da biyan tallafin man.
A wasu sassan Najeriya ma, an fara ba da rahotannin samun karin kudin man fetur din a gidajen mai, ko da yake, har yanzu ba a ji wani bayani daga hukumomin Najeriya a kan wannan batu.
Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur a cikin jawabinsa na kama mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, lamarin da ya haddasa hauhawar farashi da matsin rayuwa.