Hukumar ƙididdiga ta kasa ta ce, hauhawar farashin kayayyaki ta yi tashi mafi muni da ɓata taɓa yi ba cikin shekara 20 kashi 28.2 cikin 100 a watan Nuwamba.
A rahoton da hukumar ta fitar yau Juma’a, ta ce hauhawar farashin ta ƙaru zuwa kashi 28.20 saɓanin watan Oktoba da ya ke kashi 27.33.
Hukumar ta ce “tashin farashin kayan masarufi na shekara zuwa shekara ya faru ne sakamakon ƙaruwar farashin biredi da dankali da doya da kifi da nama da kayan itatuwa da gahawa da shayi da kuma cocoa,”
A wata bayan wata kuma, hauhawar kayan masarufi a Nuwamba ya kai kashi 2.42 cikin 100, ya ƙaru da kashi 0.51 idan aka kwatanta da yadda yake a Oktoban 2023 da yake kashi 1.93 cikin 100.