fidelitybank

Farashin kayan masarufi sun hau a watan Satumba – NBS

Date:

Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kididdiga ta kasa, NBS, ta bayyana cewa farashin kayan abinci masu mahimmanci da suka hada da wake, kwai, burodi, shinkafa da tumatur, sun samu hauhawar ƙarin farashi a watan Satumban 2024.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na zababbun duban farashin abinci na Satumba 2024 da aka fitar a Abuja ranar Laraba.

Rahoton ya ce matsakaicin farashin 1kg na wake ya karu da kashi 281.97 daga N716.97 da aka samu a watan Satumbar 2023 zuwa N2,738.59 a watan Satumban 2024.

Ya kara da cewa matsakaicin farashin kwai masu matsakaicin girma (guda 12) ya karu da kashi 137.43 a duk shekara daga N1,047.47 da aka samu a watan Satumbar 2023 zuwa N2,487.04 a watan Satumban 2024.

A cewar ofishin, matsakaicin farashin biredi ya karu da kashi 115.74 a duk shekara daga N708.36 a watan Satumbar 2023 zuwa N1,528.19 a watan Satumban 2024.

“A duk wata, kilo 1 na wake ya karu da kashi 6.37 a watan Satumba daga N2,574.63 da aka samu a watan Agustan 2024.

“A kowane wata, kwai ya karu da kashi 8.46 bisa dari daga N2,289.19 da aka rubuta a watan Agustan 2024.

“A kowane wata, farashin ya karu da kashi 4.68 daga N1,459.85 da aka rubuta a watan Agustan 2024,” in ji rahoton.

Bugu da kari, NBS ta ce matsakaicin farashin shinkafar gida ya tashi da kashi 152.92 bisa dari a duk shekara daga N757.06 a watan Satumban 2023 zuwa N1,914.77 a watan Satumban 2024.

Hakazalika, ta ce matsakaicin farashin naman shanu mara kashi 1kg ya karu da kashi 99.99 a duk shekara daga N2,816.91 a watan Satumban 2023 zuwa N5,633.60 a watan Satumban 2024.

NBS ta ce matsakaicin farashin tumatir kilo 1 kuma ya karu a duk shekara da kashi 152.94 daga N 565.69 da aka samu a watan Satumbar 2023 zuwa N1,430.87 a watan Satumban 2024.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp