Wani sabon rahoto da hukumar kididdiga ta ƙasa NBS da ta fitar, ya nuna cewa, farashin wasu kayan abinci ya karu da kashi 42 cikin dari a shekara daya a kasar nan.
Rahoton, wanda aka yi wa lakabi da “Sanya ido kan wasu kayan abinci zuwa watan Afrilun 2022” ya bayyana cewa, farashin kilogiram daya na wake (fari da baci) ya tashi da kashi 44.32, wato daga Naira 359.64 a watan Afrilun 2021 zuwa Naira 519.05 a watan Afrilun 2022.
Kazalika farashin kilogiram daya na doya ya tashi da kashi 42.88, daga Naira 252.80 a watan Afrilun 2021 zuwa Naira 361.20 a watan Afrilun 2022.
Haka kuma farashin kwalba daya na manja ya tashi da kashi 45.59, daga Naira 578.86 a watan Afrilun 2021 zuwa Naira 842.75 a watan Afrilun 2022. In ji BBC.