An kara samun hauhawan farashin kayayyaki a Najeriy, kamar yadda hukumar kididdiga ta ƙasar ta bayyana a ranar Litinin.
Rahoton na hukumar NBS ya ce an samu hauhauwar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi da ya kai kashi 16.82 cikin ɗari a watan Afrilu da ya wuce.
An samu hauhawan farashin kayayyakin a watanni uku a jere. Kuma tsadar kayayyakin ta ci gaba da lunkawa tun 2016 a Najeriya.
Tsadar man dizel da mafi yawanci ƴan Najeriya ke dogaro da shi wurin kasuwanci ya ƙara haifar da tsadar kayayyakin da kuma tasirin rikicin Ukraine.