Hukumomi a ƙasar nan, sun tabbatar da cewa, farashin kayayyaki ya hau da kashi 17.71 zuwa watan Mayun wannan shekarar.
Hakan ya sa rayuwa ta ƙara tsada, kuma ‘yan kasar na ci gaba da fama da mawuyacin hali.
Wannan yanayi ya sa jama’a da dama na ta tunanin yadda za su yi da batun sayen kayayyakin abinci ganin cewa babu kuɗi a hannunsu.
Duk da cewa, wasu jama’a sun soma matse bakin aljihu inda suke sayen abin da suke buƙata, amma duk da haka suna so su ga sun rage canji a aljihunsu idan suka shiga kasuwa sayen kayayyakin abinci.