Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta ce, farashin tikitin jirgin sama ya tashi da kashi fiye da 96 cikin 100 a cikin shekara daya.
A cikin rahotonta na watan Satumba, hukumar ta ce fasinjan jirgin sama na biyan kusan naira dubu 37 a cikin watan Satumbar 2021 amma kuma a watan Agustan bana ana biyan akalla naira dubu 65 wanda ke nuna tashin farashin tikitin.
Rahoton ya ce an samu dan karin kadan a farashin hawa motoci haya da kashi biyu cikin 100 daga shekarar da ta wuce zuwa bana.
Rahoton na hukumar NBS ta ce a bangaren sufurin babur ko kuma acaba babu wani bambamci sosai tsakanin bara da bana saboda karin bai wuce kashi daya cikin 100 ba.


