Farashin gas ya tashi a kasuwar duniya, bayan da Rasha ta rage shigar da iskar gas dinta zuwa Jamus da wasu kasashen Turai.
Farashin ya tashi da kashi biyu cikin dari a kasashen Turai. Masu suka na zargin Rasha da amfani da gas din a matsayin wani makani na siyasa.
Rasha ta katse bututunta na ‘Nord Stream Pipelines’ da ke kai wa Jamus da wasu kasashen Turai gas. kasar Jamus dai na shigar da kashi 55 cikin 100 na gas din da take amfani da shi daga Rasha