Dillalan iskar girki na gas a Najeriya, sun yi gargadin cewa farashin iskar gas mai nauyin kilogiram 12.5 na iya karuwa zuwa Naira 18,000 nan da watan Disamba idan gwamnatin tarayya ta gaza shawo kan lamarin.
Olatunbosun Oladapo, shugaban kungiyar masu sayar da iskar gas ta Najeriya ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.
Ya koka da yadda farashin iskar gas ya yi tashin gwauron zabo daga Naira miliyan 9-10 kan kowace metric ton 20 zuwa Naira miliyan 14.
Oladapo yayi kira ga hukumar da ta shigo domin duba lamarin.
A cewarsa, masu tashar tashoshin suna “boyewa da fakewa da tsadar kudaden waje domin kara farashin domin kara wa talakawa wahala.
“Akwai tashin gwauron zabi na ban dariya a halin yanzu, kuma ina fargabar cewa idan Gwamnatin Tarayya ba ta tashi tsaye wajen duba ayyukan wadannan masu gidajen man ba, farashin zai iya kaiwa har N18m kan kowace metric ton nan da Disamba. Wannan yana nufin cewa kilogiram 12.5 na iya kaiwa N18,000″, in ji shi.
Rahotanni na cewa, ana siyar da silindar gas din girki mai nauyin kilogiram 12.5 akan kudi N10,000.


