fidelitybank

Farashin fetur zai yi tashin gauron zabi – IPMAN

Date:

Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya, ta ce akwai yiwuwar nan da lokaci kaɗan farashin man fetur zai zarce naira 600 a kan kowace lita.

IPMAN ta ce hakan zai faru ne sanadiyyar rashin tabbas kan samuwar dala ga ƴan kasuwa masu shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje.

Bayanai sun nuna cewa da zarar ‘yan kasuwa masu zaman kansu suka fara shigo da man fetur a wata mai kamawa, farashin litar mai zai haura sama a faɗin ƙasar.

A lokacin da yake tabbatar wa BBC da wannan batu, shugaban ƙungiyar dillalan man fetur ɗin a yankin Arewacin Najeriya, Bashir Dan-Mallam ya ce dole ne sai gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace domin hana faruwar hakan.

Dan-Mallam ya ce samuwar dalar a wadace ga ƴan kasuwa za ta hana hauhawar farashin na litar mai.

A yanzu dai kamfanin man fetur na ƙasar NNPC ya ce zai riƙa shiga da kashi 30% na man fetur ɗin da ƙasar ke buƙata, yayin da ƴan kasuwa za su shigar da sauran.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, wani lamari da ya haifar da tashin farashin litar man fetur a faɗin ƙasar

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp