Farashin man fetur ya karye a defo-defo na Najeriya a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin ƙarin farashin man zuwa naira 700 a kan duk lita ɗaya cikin wannan wata na Yuli.
Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN ta tabbatar da karyewar farashin, ta ce ana sayar da shi a kan naira ɗari huɗu da ɗoriya, saɓanin sama da naira ɗari biyar a kan duk lita ɗaya.
Shugaban ƙungiyar reshen arewacin Najeriya, Bashir Ahmed Danmalam ya shaida wa BBC cewa farashin ya karye ne saboda ƙarancin masu saye, kuma za a samu rangwamen har a gidajen mai.
Danmalam ya ce tun kafin tafiya hutun sallah, farashin man fetur ɗin ya fara sauka.
“A yanzu haka, man fetur a defo-defo ɗin da ke Lagos da Warri da Calabar, an samu sauƙi domin ana (samun sa a kan) ƙasa da naira ɗari huɗu”.
Jami’in na IPMAN ya ce farashin man zai yi ƙasa a kwanaki masu zuwa a sassa daban-daban na Najeriya.
“A makon da muke ciki farashin zai yi ƙasa, sannan kuma ya kamata a san cewa yawan masu sayen man fetur ma ya ragu, ba kowa ne yake da kuɗin da zai iya sayen mai yanzu ba”.