fidelitybank

Faransawa sun fara zaɓen shugaban ƙasa

Date:

Faransawa na gudanar da zagayen farko na zaɓen shugaban kasa, inda za su zaɓi tsakanin ‘yan takara goma 12.

Ƴan takara biyu da suka fi yawan ƙuri’a ne za su kai ga zagaye na biyu na zaɓen nan gaba a wannan watan.

Ƴan takarar da ke kan gaba a ƙuri’ar jin ra’ayi su ne shugaba Emmanuel Macron da shugabar masu ra’ayin riƙau Marine Le Pen, waɗanda sakamakon ya nuna za su iya lashe zaɓen.

Marine Le pen ya yi ta mayar da hankali a yaƙin neman zaɓenta kan bai wa Faransa fifiko a gidaje, da ayyukan yi da kuma tsaurara matakan tsaro.

Mista Macron da ya fi mayar da hankali kan yaƙin Ukraine, sai daga baya ne ya fara taɓo batutuwan da suka shafi cikin gida.

Idan har Macron ya lashe zaɓen zai kasance shugaba na farko, bayan Jacques Chirac da ya yi wa’adi na biyu a shekaru 20.

A 2017 aka zaɓi Marcon wa’adi na farko inda ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...
X whatsapp