fidelitybank

Faransa za ta dawo wa da Najeriya dala miliyan 150 da Abacha ya sace – Tinubu

Date:

Fadar shugaban ƙasa ta ce, Faransa za ta dawo wa Najeriya dala miliyan 150 na kuɗin da tsohon Shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Sani Abacha ya sata.

Fadar shugaban ƙasar ta bayyana haka ne a yau Juma’a lokacin da shugaba Tinubu ya karɓi bakuncin ministar Turai da harkokin wajen Faransa, Catherine Colonna, a fadarsa da ke Abuja.

Tinubu ya ce ya ji daɗin labarin dawowa Najeriya kuɗin Abacha da Faransa ke shirin yi, inda ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen samar da ci gaba a ƙasar.

Shugaban ya kuma yi farin ciki da irin ƙaruwar hulɗar dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman ma a ɓangaren sauyin yanayi, ci gaban tattalin arziki, ilimi da kuma raya al’adu.

Tinubu ya kuma yaba da rattaɓa hannu kan yarjejeniyar Yuro miliyan 100 tsakanin Najeriya da Faransa don tallafawa shirin i-DICE – wani shiri na Gwamnatin Tarayya na inganta zuba jari a Fasahar Sadarwa da kuma Masana’antu na Fasaha.

Ministan sadarwa da kirkire-kirkire, Dr Bosun Tijani, da ministan harkokin kasashen waje na kasar Faransa ne suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar a wani taro da aka yi a gidan Tafawa Ɓalewa, a hedkwatar ma’aikatar harkokin wajen.

today nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp