Ministan harkokin cikin gida na Faransa ya ce ƙasar ta hana ɗan tsohon jagoran al-Qaeda, Osama Bin Laden komawa ƙasar ta Faransa.
Omar Bin Laden mai shekara 43 ya kwashe shekaru yana zaune a arewacin Faransa tare da matarsa, inda yake sana’ar zane-zane.
Ministan harkokin cikin gidan, Bruno Retailleau ya ce an hana Omar komawa ƙasar ne saboda wani rubutu a kafofin sadarwa da ke da alaƙa da tuna kashe mahaifinsa, wanda hukumomi a ƙasar suka ce yana ƙarfafa ‘gwiwar ta’addanci.’
Tun a shekarar 2023 Omar ya bar Faransa bayan an soke shaidar zamansa a sanadiyar rubutun.
A shekarar 2016 ce Omar Bin Laden ya koma zama a Faransa, bayan ya samu shaidar zama ɗan ƙasar ta hanyar auren wata ƴar Birtaniya mai suna Jane Felix-Browne, wadda ta koma Zaina Mohamed Al-Sabah.
Retailleau ya ce yanzu sun soke shaidar zamansa ɗan kasar, kuma ba sa buƙatar ya koma ƙasar ko da don wani dalilin ne.
Rahotanni na cewa yanzu ya koma Qatar ne da zama tare da matarsa. In ji BBC.
An haifi Omar ne a Saudiyya, kuma shi ne ɗan Osama na huɗu. Ya bar tafarkin mahaifinsa ne a shekarar 2000, inda ya ce shi bai amince da tsarin da ake kashe fararen hula ba.


