Faransa ta yi kiran a tsagaita wuta cikin gaggawa kuma mai dorewa a yaƙin da Isra’ila ke yi da Hamas, tana cewa ta yi matuƙar damuwa da halin da ake ciki a Gaza.
Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ce ta bayyana haka, inda ta ƙara da cewa ana kashe fararen hula da yawa da ba su ji ba ba su gani ba.
Firaiministan Isra’ila Elin Cohen ya ce tsagaita wutar zai zama kuskure, inda ya bayyana shi a matsayin wata kyauta ga Hamas.
Burtaniya da Jamus ma sun yi kira a tsagaita wutar ta dindindin, amma sun yi kiran a samar da gajeriya cikin gaggawa.
Mis Colonna ta isa Tel Aviv ranar Lahadi domin tattaunawa da takwaranta na Isra’ila Eli Cohen.
Cikin wata sanarwa da ta fitar gabanin ziyararta ta, Ministar harkokin wajen ta Faransa ta ce za ta yi kiran a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta har abada wadda za ta ƙunshi sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma shigar da kayan agaji Gaza.
Cohen ya nanata manufar gwamnatinsu ta kin tsagaita wuta.