Faransa ta tsayar tare da kwace kadarorin Oligarch na Rasha da ya kai kusan Euro miliyan 850 kwatankwacin dala miliyan 938.
An toshe kadarorin da ya kai Euro miliyan 539, in ji Le Maire Ministan Tattalin Arziki na Faransa Bruno.
Ya ce, an dakatar da wasu Euro miliyan 150 daga asusun masu zaman kansu a bankunan Faransa, an kuma kama wasu jiragen ruwa guda biyu na Yuro miliyan 150.
Yankin Turai na ci gaba da matsawa ƙasar Rasha kan mamayar da ta yi wa Ukraine.