Manyan ƙasashen duniya na cigaba da mayar da martani kan juyin-mulkin Gabon – Rasha ta ce ta damu mutuƙa kan halin da ake ciki a ƙasar.
Sannan Faransa ta sake jadadda damuwarta kan yanayin da aka shiga a Gabon; wata sanarwa da Ministan harkokin waje Olivier Véran ya fitar na cewa gwamnatinsu nason a mutunta sakamakon zaɓen da aka kammala a Gabon.
Shugaba Ali Bongo, mai shekara 64, ya lashe zaɓen kasar a karo na uku wanda aka gudanar a ranar Asabar. Sojoji a yanzu sun ce sun yi masa ɗaurin talala.


