fidelitybank

Fani Kayode ya kai karar tsohuwar matarsa kotu da yunkurin kisa

Date:

Tsohuwar matar tsohon ministan sufurin jiragen saman, Femi Fani-Kayode, ya maka tsohuwar matarsa Precious Chikwendu, a kotu da zarginta da kiransa da mai karamin azzakari kuma ta yi yunkurin hallaka shi da sabuwar budurwarsa.

Ya kara da bayyana cewa, sun yi amfani da yanar gizo wurin wallafa karairayi a kansa, inda ta ce, ya na duka tare da lalata da ‘yan aikinsa.

Jaridar Dailytrust ta rawaito cewa, ‘yan sandan sun gurfanar da Chikwendu a gaban mai shari’a, Inyang Ekwo kan zargin yunkurin kisan kai.

A karar mai lamba FHCABJ/CR/1/2022 wacce kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayyan ya shigar a kan Chikwendu da wasu mutum 3, an ce tsohuwar matar ta yi yunkurin soka wa Fani-Kayode wuka a ranar 24 ga watan Nuwamban 2018 a Asokoro.

Sauran wadanda aka gurfanar tare da Chikwendu sun hada da Emmanuel Anakan, Prisca Chikwendu da Osakwe Azubuike yayin da sauran ba a kamo su ba.

A zargi 13 da aka shigar, wadanda ake zargin a na tuhumarsu ne da laifuka da suka hada da hantara, yunkurin kisan Fani-Kayode da yunkurin kashe wata Lauretta wanda hakan yasa ta bar mu’amala da Fani-Kayode. A na zarginsu da yin amfani da shafin sada zumunta wajen aika sakonni cin zarafi da niyyar hantara da bata sunan tsohon mijinta.

Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zarginsu da su wadanda abun hukuntawa ne a karkashin sashi na 392 na dokokin Penal Code.

Mai shari’a Ekwo ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 Afirilu, 28 Afirilu da 29 Afirilu.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp