Kungiyar Flamingos ta Najeriya za ta kara da Colombia a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekaru 17 ta 2022.
Colombia ta samu gurbin zuwa zagaye na hudu na karshe bayan da ta doke Tanzania da ci 3-0 a wasan daf da na kusa da na karshe a ranar Asabar da yamma.
Kungiyar Flamingos za ta fafata da Colombia domin neman gurbin zuwa wasan karshe a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba.
‘Yan matan Najeriya sun doke Amurka da ci 4-3 a bugun fanariti a ranar Juma’a inda suka samu tikitin shiga gasar.
An tashi wasan ne 1-1 bayan mintuna 90.
Bangaren Bankole Olowookere na iya kara samar da tarihi ta hanyar tsallakewa zuwa wasan karshe.